Wannan dai wasa shi ne na zagayen farko a wasannin mako na 3 da kungiyoyin suka buga. A wannan karo Najeriyar ce ta fara bude zura kwallo a ragar Red Devils ta Congo, cikin minti na 48 ta hannun dan wasan ta Junior Ajayi, sai kuma kwallon Ajayin ta biyu, wadda ya zura mintuna 6 bayan kwallon farko. Amma kafin a tashi daga wasan itama Congo ta jefa kwallo daya a ragar Najeriya cikin minti na 66.
Game da sakamakon wasan, kocin Congo Claude Leroy, ya ce za su yi iyakacin kokarin su, su takawa Najeriya birki, a yunkurin ta na shiga gasar nahiyar ta Afirka mai kunshe da kasashe 8, wadda za ta gudana nan da karshen wannan shekara.
Leroy ya ce sakamakon wasan da ya gudana 2 da 1, ba wani abun damuwa ba ne ga kungiyar sa, kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen sauya sakamakon a wasan su na gaba.
Shi kuwa a nasa bangare kocin Najeriya Samson Siasia, cewa ya yi dalilin kwarin gwiwar su shi ne 'yan wasan sa na yawan samun nasara a waje, duba da yadda suka lashe wasan su a gidan Gabon da ci 4 da 1, kana sun doke Zambia a gidan ta da ci 2 da nema, lokacin da suke neman gurbin buga gasar matasa ta birnin Brazzaville.
Ya ce duk da 'yan matsaloli da suka fuskanta a yayin karawar su da Congo, a gaba za su yi iyakacin kokarin su wajen sake lashe wasan zagaye na biyu.(Saminu Alhassan)