in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ronaldinho zai iya buga kwallo a Switzerland
2015-10-15 09:34:06 cri
Wata kafar yada labaru ta kasar Brazil ta ba da labarin cewa, shahararren dan wasan Brazil Ronaldinho ya samu gayyata daga wani kulob din kasar Switzerland.

Jaridar 'The Lancenet news portal' ta fitar da wannan labari, tare da bayyana cewa Ronaldinho mai shekaru 35 a duniya, wanda ya taba lashe kofin duniya da na Champions League, ya taba janyo hankalin kulob din kasar Malaysia Pahang FA. Sai dai a cewar Joe Ze Mira Ferreira, wani dan kasuwan kasar Portugal, wanda ke aiki a matsayin manzon kulob din Pahang FA na kasar Malaysia, ya samu sanyin gwiwa bayan da ya yi hira da dan uwan Ronaldinho kuma wakilinsa, Roberto Assis.

An ruwaito Ferreira na cewar, wani kulob ya yi alkawarin baiwa Ronaldinho albashin da ya kai Euro miliyan 10 cikin shekara guda, kudin da kulob din Pahang FA ya kasa biya. A cewar Ferreira, kulob din da yake neman samun Ronaldinho yana kasar Switzerland. Haka zalika an ce, dan uwan Ronaldinho Assis ya taba buga kwallo a FC Sion na kasar Switzerland tsakanin shekarun 1990.

Yanzu Ronaldinho ya kasance wani dan wasa mai 'yanci, wato ba ya cikin ko wane kulob, bayan da ya janye jiki daga Fluminense na kasar Brazil a watan da ya gabata. Sa'an nan cikin watanni 3 da suka wuce, Ronaldinho ya samu halartar wasanni 9 kadai.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China