Wannan nasarar da kungiyar Jamus din ta samu a wasan share fagen a gasar cin kofin nahiyar Turai, ya tabbatar da matsayinta na farko a rukunin D wato na 4 kenan. Hakan ya kasance karo na 12 a jere da kungiyar Jamus ta samu nasarar halartar babbar gasa a nahiyar Turai.
A yayin wasan, wanda ya gudana a daren ranar Lahadin nan, 'yan wasan Jamus sun yi ta kokarin kai farmaki gidan kungiyar Georgia, yayin da Georgia ta fi mai da hankali wajen tsaron gidan ta, amma duk da haka, kungiyar Jamus ta yi nasara zara kwallaye har 2. Sakamakon wasan da aka samu, ya sa babban kocin kungiyar Jamus mista Joachim Loew ya nuna rashin gamsuwarsa cewar, 'yan wasansa sun yi ta zubar da damammaki masu yawa a yayin gasar, kuma ba su taka rawa ta azo a gani ba a wannan karo. Amma duk da haka, kocin ya bayyana cewar ya ji dadi kasancewar kungiyarsa zata samu damar halartar gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar ta 2016.(Bello Wang)