in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Neymar na jin dadin kasancewa a kulof din Barcelona
2015-10-15 09:35:02 cri
Dan wasan gaban kulof din FC Barcelona Neymar ya yi hira da wakilin shafin yanar gizo na kulof din, inda ya ce ya riga ya canza salonsa a yayin buga kwallo a wasanni daban daban.

Dan wasan dan asalin Brazil ya shiga shekara ta 3 yana taka leda cikin Barcelona, duk da cewa a lokacin zafin bana ya ba mutane mamaki bisa hira da wakilan kulof din Manchester United, sai dai a cewarsa kulof din Birtaniya bai nuna aniyar neman samunsa ba a lokacin.

Dan wasan mai shekaru 23 a duniya, wanda ya halarci wasanni kimanin 100 a madadin Barca, ya ce bayan da ya sauya sheka zuwa Barcelona, ya kwantar da hankalinsa, kuma ya daina aikace-aikacen irin na yara da ya saba yi a baya. A cewarsa, yanzu ya canza salonsa na buga kwallon kafa, da na zaman rayuwa, bisa samun taimako daga wajen kulof din Barcelona.

A yayin kakar wasansa ta farko a Barcelona, Neymar ya fuskanci wahala sosai, ganin yadda kulof din wanda a lokacin ke karkashin jagorancin Tata Martino, ya yi kokarin daidaita tsarinsa, har ma ya mika kambi ga Atletico Madrid. Amma yanayin ya daidaita a bara, bayan da Luis Enrique da Luis Suarez suka halarci kungiyar Barca.Wadannan 'yan wasa 2 da Neymar da Leo Messi sun zama tamkar wani gungu ne na masu kwarewa wajen kai hari ga gidajen abokan karawarsu, lamarin da ya mayar da Barca matsayin zama kan gaba a cikin gida gami da nahiyar Turai baki daya.

A cewar Neymar, 'yan wasan Barca sun nuna wani yanayi mai kyau a kakar wasa da ta gabata, ban da haka kuma shi da Messi da Suarez sun kulla abokantaka, abin da ya sabawa tunanin wasu mutane da yawa, wadanda suka dauka cewar ba za a samu jituwa ba tsakanin wadannan 'yan wasa.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China