Shugaba Muhammad Buhari, shi ne ya ayyana nadin sabon shugaban yayin zaman majalisar zartaswar kasar na wannan mako.
Gwamnan jihar Sokoto shiyyar arewa maso yammacin kasar Aminu Waziri Tambuwal, ya ce nada sabon shugaban ya yi dai dai da dokokin kundin tsarin mulkin Najeriya da ita kanta majalisar zartaswar kasar.
Farfesa Attahiru Jega, shi ne tsohon shugaban hukumar wanda ya yi murabus bayan karewar wa'adin aikin sa a watan Yuni bayan shafe shekaru 5 yana jan ragamar shugabancin hukumar, kuma a karkashin mulkinsa ne hukumar zaben kasar ta gudanar da sahihin zabe wanda ba'a taba samun sa ba a tarihin kasar cikin wannan shekara da muke ciki.
Zaben na watan Maris na shekarar 2015, shi ne irinsa na farko a tarihin kasar inda shugaba mai ci ya sha kaye daga abokin hamayyrsa a zaben kasar wacce ta fi yawan al'umma a nahiyar Afrika.(Ahmad Fagam)