in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojin Najeriya ta kubutar da iyalai 16 daga hannun boko haram a arewa maso gabashin kasar
2015-10-22 09:43:17 cri
Rundunar Sojin Najeriya sun tabbatar da hallaka 'yan tsageran boko haram guda biyu sannan suka kubutar da iyalai 16 a garin Madagali dake jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar.

Babban kwamandar rundunar mai kula da bataliya ta 28 dake Mubi a cikin jihar Manjo Janar V.O.Ezugwu ya shaida ma manema labarai ta wayar tarho cewa an samu wannan nasara ne a ranar talatan wannan makon a lokacin wani arangama da 'yan kungiyar a karamar hukumar na Madagali.

Janar Ezugwu ya ce fiye da shanu 100 aka kwato da bindogogin AK47 guda 2, da gurneti 6, da bindigogi masu sarrafa kansu guda 2 da baburan hawa 18 daga hannun 'yan kungiyar da suka tsere.

Ya tabbatar da cewa nan take aka lalata baburan sannan ya yaba ma kokarin 'yan banga dake yankin saboda irin gudunmuwa da hadin kai da suka ba sojojin.

Kungiyar ta boko haram dai kwanan nan ta kai hari a wassu kauyuka dake garin na Madagali.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China