in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD ya yi kira da a hana tsanantar rikicin jin kai a kasar Sham
2015-07-29 10:48:49 cri

Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai kuma jamai'in kula da ayyukan jin kai na gaggawa Stephen O' Brien ya bayyana a jiya Talata cewa, rikicin kasar Sham ya haifar da illa ga manufofin jin kai na kasa da kasa.

Abu mafi muhimmanci da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne samo hanyar kawo karshen rikicin kasar ta yadda ba zai kawo cikas ga ayyukan jin kai a kasar ba.

Stephen O' Brien ya jaddada a yayin da ya mika rahoto kan yanayin da kasar Sham ke ciki ga taron kwamitin sulhu na MDD a wannan rana cewa, daga lokacin da rikicin kasar Sham ya barke zuwa wannan lokaci, mutane fiye da dubu 220 ne suka mutu, kana mutane miliyan 8.6 suka rasa gidajensu, a sakamakon haka, mutane fiye da miliyan 12 suna bukatar tallafin jin kai.

Bugu da kari, Stephen O' Brien ya kuma zayyana mummunan tasirin da kungiyar IS ta haifar ga kasar Sham. Yana mai jaddada cewa, rikicin ya wargaza tsarin zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasar ta Sham da kuma sakamakon da aka samu wajen raya kasa.

Bayanai na nuna cewa, kashi 80 cikin dari na al'ummar kasar Sham suna fama da talauci.Don haka ya yi kira ga kasashen duniya da su hanzarta lallubo hanyoyin warware rikicin kasar ta Sham.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China