in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da yadda aka tarwatsa wani tsohon gidan ibada a kasar Sham
2015-08-25 10:46:27 cri

Babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ba da sanarwa a jiya Litinin, inda ya yi Allah wadai da yadda kungiyar IS ta tarwatsa wani tsohon gidan ibada a kasar Sham, kana ya yi kira ga kasashe dabam daban da su yi kokarin hana kai irin wannan farmakin ta'addanci.

A cikin sanarwar, Ban Ki-Moon ya yi allah-wadai da yadda kungiyar IS ke ci gaba da aikata ayyukan ta'addanci da kuma keta dokokin kasa da kasa a kasar Sham, ciki har da lalata da kuma kwashe kayayyakin tarihi da dama a kasar Sham.

Sanarwar ta ce, a cikin shekaru 4 da suka gabata,'yan ta'adda sun kai hari kan fararen hula tare da lalata kayayyakin al'adu na tarihi a kasar Sham. Ban Ki-Moon ya nanata cewa, lalata kayayyakin tarihi babban laifin yaki ne, kuma dole a hukunta wadanda suka aikata wannan laifi.

Shugaban babban dakin ajiye kayayyakin tarihi na kasar Sham ya bayyana a jiya Litinin cewa, dakarun kungiyar IS sun tarwatsa tsohon gidan ibada na Baal shamin dake garin Ted Moore da boma-bomai a ranar Lahadin makon da ya gabata. Garin Ted Moore dai yana da nisan kilomita 215 daga yankin arewa maso gabashin birnin Damascus, babban birnin kasar Sham, inda gine-gine tun zamanin daular Roma na shekaru fiye da dubu 2 suke, kuma kungiyar UNESCO ta mai da shi daya daga cikin kayayyakin al'adun tarihi na duniya a shekarar 1980.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China