in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin gwamnatin Sham sun hallaka dakarun kungiyar Al-Nusra Front
2015-07-21 11:19:00 cri

Kamfanin dillancin labaru na kasar Sham, ya bayyana cewa sojojin gwamnatin kasar sun kaddamar da hare-hare a wurare da dama, inda suka samu nasarar hallaka dakarun kungiyar Al-Nusra Front da dama.

An ruwaito jami'in rundunar sojan kasar na cewa, sojojin gwamnati sun dauki matakan soja kan sansanonin kungiyar dake jihar Hama, da jihar Idleb dake arewacin kasar, inda suka hallaka dakaru a kalla 50. Ban da haka kuma, sojojin sun harbe dakaru a kalla 38 a yankin karkarar dake arewa maso yammacin birnin Hama, fadar mulkin jihar Hama, ciki har da madugan kungiyar su biyu.

Bugu da kari, labarin ya ce, a wannan rana, sojojin gwamnatin kasar da kuma jam'iyyar Hezbollah ta kasar Lebanon, sun cimma nasarar daukar matakan soja a birnin Zabadani dake yankin iyakar kasashen biyu, inda suka mamaye wurare da dama dake birnin, tare da yanke hanyoyin sufurin kayayyaki na kungiyar masu tsattsauran ra'ayi.

Wani jami'in rundunar sojan kasar ya ce, dakarun ciki har da wani madugunsu, sun rasa rayukansu a sakamakon hare-hare ta sama, wanda sojojin gwamnatin kasar ta Sham suka kaddamar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China