in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai wani sabon harin kunar bakin wake a Najeriya
2015-10-16 20:47:59 cri
Rahotanni daga tarayyar Najeriya ya tabbatar da cewar a kalla mutane 7 ne suka mutu a Jumma'an nan sakamakon wani sabon harin kunar bakin wake a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, kamar yadda jami'in ba da agajin gaggawa a jihar ya bayyana, kwana daya bayan abkuwat irin wannan harin a wani masallacin unguwa a birnin.

Wadansu mata 3 ne suka ta da bam din dake daure a jikinsu a safiyar Jumma'an nan a wata unguwar da ake kira Umarari Bayan Waya kusa da Maiduguri, babban birnin jihar wanda ya yi sanadiyar jikkar mutane 10, in ji jami'in na hukumar ba da agajin gaggawa na yankin, Abdulkarim Ibrahim.

Wannan ya kawo adadin wadanda suka mutu a harin kunar bakin wake zuwa 36 a cikin yini biyu

Tun da farko ma'aikatan ba da agajin gaggawa sun ce mutane 29 ne suka mutu tsakanin Alhamis zuwa yau Jumma'a.

'Yan sanda sun tabbatar da hakan suna mai bayanin cewa wadanda harin nan ya rutsa da su suna salla ne lokacin da aka ta da bam din a cikin masallaci a Molai wani waje dake wajen Maiduguri, abin da ya sa masallacin rushewa gaba daya.

Harin ranar Jumma'an nan kuma shi ne na uku a cikin makon nan duk a garin na Maiduguri bayan wani mummunan harin da ya auku a ranar Talata ya hallaka mutane 8.

Ana zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai wannan harin. Kungiyar dai sun ce suna son hambarar da gwamnatin kasar ne su kafa daular musulunci, inda ya zuwa yanzu suka kai hare-hare da dama a yankin arewa maso gabashin kasar da kuma babban birnin tarayyar a cikin 'yan shekarun nan.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurni ga rundunar tsaron kasar da su tabbatar da sun kakkabe kungiyar nan da watan Disamban karshen shekara. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China