in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na kwalejojin Confucius a kasar Birtaniya
2015-10-23 09:02:08 cri

A jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron shekara-shekara na kwalejojin Confucius a kasar Birtaniya tare da Yarima Andrew a birnin London.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, kasancewar gadar dake hada al'adu da harsunan kasar Sin da kasashen waje, kwalejojin Confucius sun taka rawa mai armashi ga mutanen dake nuna sha'awa ga al'adun Sinawa da yaren Sinanci wajen koyon yaren da kara sanin al'adun Sinawa, kuma sun ba da gundummawa sosai wajen kara musayar ra'ayi a fannin al'adu a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya.

Bugu da kari, Xi ya bayyana cewa, a shekarun baya, kwalejojin Confucius sun samu bunkasuwa sosai a Birtaniya. A halin yanzu, kasar Birtaniya ta kafa kwalejojin Confucius 29, kuma su ne mafi yawa idan aka kwantanta da sauran kasashen Turai.

A nasa bangaren, Yarima Andrew ya yi jawabi a matsayin sa na dadadden aboki ga kasar Sin, ya ce ya goyi bayan bunkasuwar kwalejojin Confucius, kuma yana fatan sauran yara 'yan Birtaniya za su koyi Sinanci. A cewarsa kasar Sin kasa ce mai muhimmanci sosai a duniya, hulda a tsakanin kasashen Birtaniya da Sin na da muhimmanci. Za a iya ba da gundummawa ga bunkasar huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu ne ta hanyar koyon Sinanci.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China