in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping da Uwargidan sa sun gana da mai jiran gadon sarauta na Birtaniya Charles
2015-10-21 09:25:17 cri

A jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da Uwargidansa Madam Peng Liyuan suka gana da mai jiran gadon sarautar Birtaniya Yarima Charles da matarsa Madam Camilla a birnin London.

Haka kuma sun saurari wake-waken Wales tare da kallon zane-zane da kayayyakin sassaka da rubuce-rubucen da daliban kasar Sin dake karatu a kasar Birtaniya suka yi. Bayan wannan bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi na sada zumunta.

A lokacin tattaunawar su Shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen Sin da Birtaniya kasashe ne masu kawo babban tasiri ga duniya, kuma huldar dake tsakaninsu tana da muhimmanci sosai, ba ma kawai ta shafi kasashen biyu ba, hatta ma ta haifar da tasiri ga duk duniya. Ya lura cewa a cikin shekarun baya, Masarautar Birtaniya ta dora muhimmanci sosai kan bunkasuwar huldarsu, tare da ba da babbar gundummawa ga bunkasuwarta, abin da ya sa ya bayyana godiya akan hakan.

A nasa bangare, Yarima Charles mai jiran gadon sarautan kasar ta Birtaniya ya yi maraba da isowar Shugaba Xi Jinping, tare da bayyana fatan zai cimma nasarar yin wannan ziyarar aiki, domin kara neman samun bunkasuwar huldar kasashen biyu.

Ban da haka kuma, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayi a fannonin neman samun bunkasuwa mai dorewa da sauyawar yanayi da yin tsimin makamashi da kuma makamashi masu tsabta, suna ganin cewa, ya kamata a karfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a wadannan fannoni.

Har ila yau a lokacin wannan ziyara Shugaban kasar na Sin, Xi Jinping ya gana da Yarima Charles a fadar Buckingham.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China