in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar wasan kwallon kafa ta Jamus ta musunta labarin da aka bayar cewa, wai ta taba baiwa FIFA cin hanci
2015-10-22 16:24:58 cri
Bisa labarin da mujallar Spiegel ta kasar Jamus ta bayar a kwanakin baya, an ce, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Jamus ta samu iznin daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006 bayan da ta baiwa hukumar FIFA cin hanci, amma hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Jamus ta musunta wannan rahoto.

Rahoton ya bayyana cewa, yayin da kasar Jamus take neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006, hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Jamus ta baiwa wasu jami'an kwamitin gudanarwa na hukumar FIFA cin hanci, wannan ya sa kasar Jamus ta samu muhimman kuri'un goyon baya hudu daga jami'an hukumar ta FIFA.

Game da wannan batu, shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Jamus Wolfgang Niersbach ya tabbatar a gun taron manema labaru da aka gudanar a ranar 19 ga wata cewa, ba su taba baiwa hukumar FIFA cin hanci ba, sun shiga takarar neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya bisa gaskiya da adalci.

Ministan harkokin cikin gida na kasar Jamus Otto Schily ya bayyana cewa, bai ga wasu muhimman shaidu da ke nuna cewa, hukumar wasan kwallon kafa ta Jamus ta bayar da cin hanci ba. Kana lauyan hukumar Christian Schertz ya bayyana cewa, hukumar za ta gurfanar da mujallar Spiegel a gaban kotu, inda za ta bukaci mujallar da ta biya ta saboda bata mata suna

A halin yanzu, hukumar FIFA ta fara yin bincike kan wannan batu. Kana hukumar gabatar da karraki ta kasar Jamus za ta gudanar da bincike game da wannan zargi da ake yiwa hukumar kwallon kafan kasar.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China