Ahmed ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, muhimmin aikin tawagar sojojin Sudan shi ne taimakawa Yemen wajen tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta'addanci a karkashin jagorancin sojojin hadin gwiwa.
Kana ya ce, sojojin hadin gwiwa sun bude kofa ga dukkan sojojin kasashen Larabawa don taimakawa gwamnatin Yemen da zummar samun zaman lafiya mai dorewa a kasar.
Bisa labarin da sojojin hadin gwiwa suka bayar, an ce, tawagar sojojin Sudan ta yi sansani ne a manyan unguwannin birni Aden gabannin isowarsu don taimakawa wajen aikin tabbatar da tsaro.
A watan Yuli na bana, sojojin gwamnatin kasar Yemen masu goyon bayan shugaban kasar Abd-Rabbu Mansour Hadi, da dakarun kabilu sun kwace Aden daga hannun dakarun Shiite Houthi da sojojin tsohon shugaban kasar Salih wadanda suka mallaki yawancin yankunan kasar. Daga baya, gwamnatin Yemen ta yi hijira zuwa Aden daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya, amma ba a sassauta halin da ake ciki ba a Aden. (Zainab)