in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin bom ya hallaka mutane 15 a kusa da babban birnin Najeriya
2015-10-03 17:49:16 cri
Jami'an Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane 15, sannan wasu 39 sun jikkata sakamakon harin bom wanda ya afku a ranar Jumma'ar nan a kusa da babban birnin kasar.

A Nyanya, harin ya kashe mutane 2 ne, sannan ya raunata wasu 19. Yayin da a kauyen Kuje dake kusa da birnin na Abuja harin ya kashe mutane 13 da kuma raunata wasu 20.

Jami'in hukumar ba da agaji ta NEMA Ishaya Chonoko, ya tabbatar da wannan adadi.

Ya ce tuni aka kwashe gawawwakin wadanda suka mutu da wadanda suka samu munanan raunuka zuwa babban asibitin Asokoro dake Abuja.

Kwamishinan 'yan sandan babban birnin Wilson Inalegwu, shi ma ya tabbatar da faruwar harin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China