in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 14 suka mutu 39 kuma suka jikkata a jerin harin bam a Najeriya
2015-10-03 13:13:02 cri
Rahotanni daga Nigeriya ya tabbatar da cewar a kalla mutane 14 suka mutu wadansu 39 kuma suka ji rauni a wassu jerin harin bama bomai da suka auku a garin Maiduguri na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Fashewar a wurare hudu a jere suka auku a garuruwan Sajeri da Dalla a cikin jihar a ranar Alhamis, in ji kakakin sojin yankin kanar Usman Sani Kukasheka.

Harin bam din na kunar bakin wake da 'yan kungiyar Boko Haram suka saka cikin rigunansu kafin su tayar da shi ya auku ne a gaban masallacin unguwa, kamar yadda wani jami'in asibiti ya tabbatar karuwar wadanda suka mutu zai iya yiwuwa saboda wadansu da suka ji rauni suna cikin mawuyacin hali.

Wadannan tagwayen harin bam din ya zo ne bayan murnan da aka yi ta yi na cewar 'yan kungiyar su 80 sun mika wuya ga rundunar sojin jihar.

A cikin wata sanarwa daga rundunar sojin an ce wadanda suka mika wuya sun hada da wassu kwamandojinsu, da masu samo musu kayayyakin aiki da kuma masu kawo musu rahotanni. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China