Hukumar kula da gandun daji ta kasar Sin ta gabatar da rahoto a yau Alhamis cewar, daga ranar 15 ga wannan wata zuwa 15 ga watan Oktoba na shekarar 2016, kasar Sin ta hana shigar da hauren giwa da aka yi farauce su a nahiyar Afirka zuwa kasar ta, kuma hukumar ta dakatar da karbar neman izni a wannan fanni.
Wani jami'in hukumar ya bayyana cewa, Sin ta dauki wannan mataki don hana farautar giwaye, sannan ta yi kira ga sauran kasashen duniya da su dauki irin wannan matakin don bada kariya ga giwawa a nahiyar ta firka. (Zainab)