Shafin yanar gizo na cinikayya na kasar Jamus ya bayyana cewa, wannan taro ne mai muhimmanci. Sabon shirin shekaru 5 na raya kasa ba kawai zai tabbatar da yadda tattalin arziki kasar Sin zai kasance a nan gaba ba, har ma zai kawo tasiri kan za a iya samun farfadowar tattalin arziki ko a'a. Gidan telebijin na NHK na kasar Japan ya bayyana cewa, shugabannin kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping suna kokarin yin kwaskwarima ga tsarin kasar, inda suka fi mai da hankali kan ingancin bunkasuwar tattalin arziki, amma ba saurin bunkasuwarsa ba. Burinsu shi ne inganta yawan GDP na kasar Sin a shekarar 2020ta yadda zai ninka sau biyu bisa na shekarar 2010. Don haka, ana mayar da hankali sosai kan sabon shirin shekaru 5 na raya kasa da shugabannin kasar za su tsara.
Jaridar Lianhe Zaobao ta kasar Singapore ta bayar da labari cewa, a yanayin da kasar Sin ke ciki na kara samun raguwar bunkasuwar tattalin arziki, an yi hasashe cewa, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin za su gabatar da sabbin manufofin sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arziki tare da rage saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar. (Zainab)