Wasan wanda ya gudana a filin wasan Aljazeera, dan wasan kasar Masar Ahmed Hassan Coca ne ya fara jefa kwallo cikin ragar Zambia bayan fara wasan da mintuna 2, sannan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci da mintuna 3, Ahmed ya sake zara kwallo ta 2 cikin raga. Daga bisani, kungiyar Masar ta tabbatar da nasararta inda ta zara kwallo na 3 cikin ragar Zambia, kuma Amr Gamal ne ya jefa kwallon yayin da ya rage minti daya kafin karkare wasan.
A cewar Kalusha Bwalya, shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Zambia, 'yan wasan Zambia ba su mai da hankali sosai ba a wannan karo, ganin yadda 'yan wasan Masar suka yi ta zara kwallaye cikin raga Zambiar. Amma duk da haka, shugaban ya ce sakamakon halartar wannan wasan, 'yan wasan Zambia sun samu damar motsa jikinsu, ta yadda zai kasance tamkar share fage ne a wasanni 2 masu muhimmaci da za su halarta a wata mai zuwa.
Zambia za ta kara da Sudan a wasanni 2 a watan Nuwamba mai zuwa don samun izinin halartar gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018. Wasan farko zai gudana ne a makon farko na watan Nuwamba, yayin da wasa na biyu za a gudanar da shi a ranar 15 ga watan.(Bello Wang)