151001-ronaldo-zai-bude-makarantun-nazarin-kwallon-kafa-a-kasar-sin-Bello.m4a
|
Ronaldo ya fadi haka ne yayin bikin kaddamar da wata makarantarsa a Campinas na jihar Sao Paulo ta kasar Brazil. Ya ce, dalilin da ya sa yake son bude makarantu a kasar Sin shi ne domin akwai masu sha'awar kwallon kafa da 'yan wasan kwallon kafa masu dimbin yawa a kasar ta Sin amma ba yana burin tara kudi ba ne. Ya lura gwamnatin kasar da kungiyoyin jama'a suna mai da hankali sosai kan raya wasan kwallo kafa. Don haka, Ronaldo ya ce yana fatan yin amfani da fasaharsa wajen taimakawa kasar Sin raya fannin wasan kwallon kafa.
A ganin Ronaldo, wasan kwallon kafa a kasar Sin yana da tushe mai kyau, kana shugabannin da jama'ar kasar suna da niyyar raya aikin, sai dai har yanzu wasan kwallon kafa na kasar ba shi da wani tsari mai kyau, kuma ba a samu fasahar ci gaba na horar da 'yan wasa ba.
A cewar mista Ronaldo, wasan kwallon kafa a kasar Sin ya riga ya zama wani abun da ya fi janyo jari daga kasashe daban daban. Haka kuma, alkaluman da aka samu daga kasuwar musayar 'yan wasa ta kasar Jamus sun nuna cewa, kulof kulof masu buga gasar kwararrun 'yan wasa ta kasar Sin sun ware kudin da ya kai Euro miliyan 108 a tsakanin shekarar 2014 da ta 2015 don samun fitattun 'yan wasa da masu horar da 'yan wasa 'yan kasashen waje.
Hakika, ta fannin yawan kashe kudi don samun kwararrun 'yan wasa kasar Sin ta yi nisa, bisa la'akari da yadda ta zama ta biyu wajen yawan kudin da aka ware, inda take bin bayan Premier League ta kasar Birtaniya. Duk da cewa an tabbatar da matsayin masu zaman kansu na kulof daban daban na kasar a shekaru 20 da suka wuce.
A makon da ya gabata, tsarin gasar kwararrun kulof kulof na kasar Sin ya sayar da iko nuna hotunan bidiyo na gasar a shekaru 5 masu zuwa, da kudin Sin Yuan biliyan 8, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1300.
A farkon shekarar nan, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da wani babban shirin raya wasan kwallon kafa a kasar, inda aka sanya burin dawo da kungiyar 'yan mata ta kasar cikin jerin kwararrun kungiyoyi mafi karfi na duniya, daga bisani kuma za a raya kungiyar 'yan wasan maza ta kasar don ita ma ta shiga sahun gaba. Haka kuma kasar Sin tana da niyyar neman daukar bakuncin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa.
Duba da yanayin da ake ciki yanzu, duk da cewa kasar Sin ta zuba jari sosai ga harkar wasan kwallon kafa, kuma tana gudanar da gyare-gyare a wannan fanni, amma kungiyar kasar ba ta taka wata rawar a-zo-a-gani ba tukuna. Zuwa yanzu kungiyar 'yan wasan maza ta kasar ta samu izinin halartar zagayen karshe na gasar cin kofin duniya karo daya kawai, wato a shekarar 2002. Yayin da kungiyar mata ta kasar ita ma tana kokarin farfado da nagartaccen yanayin da take ciki a shekarar 1999, lokacin da ta lashe lambar Azurfa a gasar cin kofin duniya ta mata.
A ganin, Carlos Wizard Martins, shugaban makarantun Ronaldo, kasar Sin za ta iya samun ci gaba sosai a kokarin samun sakamako mai kyau a gasar cin kofin duniya, bisa samun taimako daga makarantun Ronaldo.
A cewarsa, kasar Sin ta riga ta zama kasuwa mafi muhimmanci ga makarantun Ronaldo. Zuwa yanzu an riga an bude wasu makarantun koyar da fasahar wasan kwallon kafa a kasahen Amurka da Brazil, amma yawan makarantun da aka kafa a kasashen 2 ba zai kai yawan makarantun da ake shirin kafa su a kasar Sin ba.
Mafi yawa daga cikin makarantun da za a kafa a kasar Sin, a cewar Martins, za su kasance a biranen Beijing da Shanghai da kuma Shenzhen ne, inda za su yi hadin gwiwa da makarantun kasar Sin, gami da makarantun koyar da fasahar wasan kwallon kafa da ake dasu yanzu a kasar Sin. Haka kuma za a zabi wasu fitattun 'yan wasa matasa don su samu horo a kasashen Amurka da Brazil.
Martins ya ce zai raka Ronaldo ziyara kasar Sin a watan Nuwamba mai zuwa, inda za su halarci bikin bude wata makarantar koyar da fasahar wasan kwallon kafa. Har wa yau za su yi amfani da wannan dama don musayar ra'ayi tare da masu kula da wasan kwallon kafa na kasar Sin kan yadda za a karfafa hadin gwiwa tsakaninsu a nan gaba. (Bello Wang)