Iyayen dan wasan, sun sanar da haka ne wasu sa'o'i bayan da wani alkalin kasar Brazil mai suna Carlos Muta ya kwace kadarorin dan wasan wanda darajarsu ta kai Reais miliyan 189, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 47, wadanda aka ce suna karkashin mallakar kyaftin din kasar Brazil.
An zartas da hukuncin kan Neymar ne bisa zarginsa da kauracewa biyan harajin da ya kai Reais miliyan 63 tsakanin shekarun 2011 zuwa 2013, wanda ya kunshi kudin harajin da ya kamata ya biya bisa kudin da ya samu ta hanyar sauya sheka daga kulob din Santos zuwa Barcelona a shekarar 2013.
Ban da haka kuma, hukumomin kasar Brazil sun dakatar da ajiyar banki na baban Neymar, da na kamfanoninsa.
A nashi bangaren, mista Neymar da Silva Santos, wato baban Neymar, ya bayyana a wata sanarwa cewar, dansa ba shi da alaka da kamfanonin wadanda ke karkarshin bincike, don haka bai kamata ya biya haraji kan wadannan kadarori ba.
Da ma dai an ce kulob din Barcelona ya biya kudi Euro miliyan 57 don samun Neymar, amma daga bisani kulob din ya sauya maganar cewa kudin da ya kashe ya kai kimanin Euro miliyan 86.(Bello Wang)