A nashi bangare, dan wasan kulob din Zamalek Ayman Hefny, ya samu damar mayar zara kwallo daya cikin ragar Etoile, bayan da aka rigaya aka zara kwallaye 2 cikin ragar kulob din kasar Masar. Sai dai Zamalek ya tsaya a nan bai sake taka wata rawar a-zo-a-gani ba a wasan.
Idan an waiwayi wasanni 3 da aka kammala bugawa a matsayin wasannin rukunai a wannan kakar wasan, za a ga Etoile ta samu maki 4,wanda kuma yana cikin wani yanayi mai kyau da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kulob din. Yayin da a nasu bangare 'yan wasan kulob din Zamalek sun samu maki 3 kawai, inda har Orland Pirates na kasar Afirka ta Kudu ya lashe kulob din da ci 4 da 1 a wasan da ya gudana tsakaninsu makwanni 2 da suka wuce.
An samu sakamakon wasan ne wasu sa'o'i 24 bayan da Pirates ya lashe Al Ahly, wani kulob din Tunisia mai karfi ne, da ci 1 da ba ko daya, a birnin Soweto na kasar Afirka ta Kudu.(Bello Wang)