A wajen wasan da ya gudana a ranar Asabar, Messi ya samu raunin cikin mintuna 4 da fara buga wasan. Bayan da aka duba gwiwarsa, gami da yi masa jinya, Messi ya yi kokarin komawa filin wasa don ci gaba da taka leda, sai dai lamarin ya faskara domin sake komawar sa filin bai wuce mintuna 8 ba aka maye gurbin sa da dan wasan gaba Munir sakamakon jin tsananin zafi a gwiwarsa. Likitoci sun duba jikin Messi, in da suka hakikance cewar yana bukatar huta har na tsawon watanni 2.
Hakan na nufin cewa, Messi ba zai samu damar halartar wasu wasanni da kungiyar Barca za ta buga tare da kulof din Sevilla da Rayo Vallecano da Eibar da Getafe da Villarreal, karkashin tsarin gasar La Liga ba. Ban da haka kuma, watakila muhimmin wasan da ake shirin bugawa tsakanin Barca da Real Madrid a ranar 21 ga watan Nuwamba, shi ma ba zai samu halartar Leo Messi ba, sabo da mai yiwu ba zai gama murmurewa sosai ba zuwa lokacin.
Jin raunin da Messi ya samu zai zama matsi ga kulob din Barca bisa la'akari da dan wasanta Rafinha shi ma yana jinya sakamakon jin rauni, kuma ba zai halarci ko wasa guda ba a duk tsawon kakar wasannin da muke ciki.(Bello Wang)