in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO ta yi fatan kasar Sin za ta kara taka rawa a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa
2015-04-14 21:00:50 cri

Mai ba da taimako ga babban sakataren hukumar abinci da ayyukan noma ta MDD FAO Laurent Thomaz, ya ce kasar Sin, da kuma fasahohin kasar na zamani, na taimakawa kasashe masu tasowa da yawa. Kuma akwai a nan gaba akwai bukatar kasar ta Sin ta kara taka rawar gani, a fannin hadin gwiwa tsakaninta da sauran kasashe masu tasowa.

Mista Thomaz wanda ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da hukumarsa ta shirya a Talatar nan, ya kara da cewa yanzu haka, hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da hukumar FAO ta yi matukar kyautata. Kuma a nan gaba ana fatan kara hadin gwiwa a wasu muhimman fannoni, kamar rage yunwa, da tabbatar da dauwamammen karuwar hatsi.

Mista Thomaz ya ce ana fatan kasar Sin, za ta samar wa kasashe masu tasowa taimako ta fuskar fasaha, kana kuma za ta taimaka musu ta fuskar shawarwari da manufa, a kokarin more ilimi, da kyawawan fasahohi tare da kasashen masu tasowa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China