Mataimakin zaunannen wakilin Sin dake MDD Wang Min ya bayyana a jiya Talata cewa, yarjejeniyar da aka cimma game da nukiliyar Iran a dukkan fannoni za ta taimaka wajen tabbatar da hana yaduwar makaman nukiliya a duniya, da sa kaimi ga samun zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, don haka yana fatan bangarori daban daban da batun ya shafa za su aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.
Wang Min ya bayyana a gun taron kwamitin sulhun MDD kan aikin binciken kwamitin kula da sanyawa Iran takunkumi cewa, aiwatar da yarjejeniyar nukiliyar Iran a dukkan fannoni shi ne matakin farko na warware matsalar nukiliyar kasar ta Iran, don haka aiwatar da yarjejeniyar yana da matukar muhimmanci.
Lu Kang ya bayyana cewa, Sin tana fatan bangarori daban daban za su yi kokari tare don sa kaimi ga kasar Iran ta kara baiwa hukumar IAEA hadin kan da ya kamata. (Zainab)