Jaridar kayhan ta kasar Iran ta ba da sharhi a ranar Asabar cewa, jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Sayyed Ali Khamenei ya nuna adawa ga yarjejeniyar nukiliya da aka kulla a watan da ya gabata.
Babban edita na jaridar kayhan Hossein Shariatmadari ya rubuta wannan sharhi, wanda ya jawo hankula sosai bayan da aka gabatar da shi, musamman ma ta la'akari da yadda Shariatmadari yake da hulda mai kyau tare da Ali Khamenei. Hossein Shariatmadari ya ce, yarjejeniyar ta kawo illa ga mulkin kai da tsaro na kasar Iran da kuma tsarin Islama da kasar ke bi.
Ali Khamenei ya yi jawabi a watan Yuli cewa, ba za a yarda a keta ka'idoji masu tushe na tsarin Islama ba, ko da an zartas da yarjejeniyar nuliliya ko a'a. Hossein Shariatmadari ya bayyana cewa, hakan ya bayyana cewa, shugaban kasar bai gamsu sosai ba da wannan yarjejeniya.
Tun da aka kulla yarjejeniyar nukiliya a watan da ya gabata, duk da cewar, Ali Khamenei ya nuna godiya ga kwamitin dake kula da shawarwarin nukiliya, amma bai nuna ra'ayinsa kan yarjejeniyar ba.
Bayan da aka yi shawarwari cikin dogon lokaci, kasar Iran da kasashe 6 da batun nukiliya ya shafa sun kulla yarjejeniyar nukiliya a dukkan fannoni a watan da ya gabata. Kasar Iran za ta kayyade shirinta na nukiliya bisa yarjejeniyar, sa'an nan a nata bangare, kasar Amurka za ta soke takunkumin da aka kakkabawa kasar Iran.(Lami)