Parchin yanki ne mai matukar muhimmancin gaske kan batun shirin nukilyar Iran, wanda hukumar ta IAEA ke dauka a matasayin wata ma'ajiya ce ga shirin nukilyar kasar, kuma hukumar ta IAEA tana bukatar a gudanar da bincike ne a tsanaki a yankin maimakon a dauki saufuri.
Sanarwar ta kara da cewar babban daraktan hukumar ta IAEA Yukiya Amano da kuma shugaban sashen kiyaye haddura na hukamar Tero Varjoranta sun ziyarci yankin ne bisa yarjejeniyar da aka kulla kan batun nukiyar Iran.
Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin haske kan batun ba.
A ranar Lahadin ne Amano ya gana da shugaban kasar Iran Hassan Rauhani da shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta Iran Ali Akbar Salehi, da kuma ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif a Tehran babban birnin kasar.
Ziyarar jami'an dai ta zo ne a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar hukumar ta IAEA da aka kulla tun awatan Yuli a taron manyan kasashen duniya don warware takaddama kan batun shirin nukiyar kasar Iran. (Ahmad Fagam)