A yayin bude taron, shugaban kasar Omar al-Bashir ya bayyana da farko cewa, ya kamata shimfida yanayin siyasa na zaman lafiya da na yanayin zamantakewar al'umma mai 'yanci a kasar, idan ana son cimma burinmu na samun farfadowar kasar Sudan daga dukkan fannoni, kana, ya kara da cewa, za a ci gaba da bude kofar yin shawarwarin zaman lafiya, ana kuma maraba da halartar sauran wadanda ba su shiga ba halin yanzu.
Wakilai guda 92 suka halarci taron, wadanda suka zo daga jam'iyyar mai mulkin kasa ta NCP, galibin jam'iyyun adawa da kuma kungiyar dakaru ta Darfur. Amma ba a samu halartar wakilan kungiyar neman 'yancin al'ummomin kasa ta SPLM da kungiyar Umma da wasu kungiyoyin adawa a taron ba.
Haka kuma, shugaban kasar Chadi ya halarci taron a madadin mai shiga tsakani na gwamnatin kasar Sudan da kungiyoyin adawa.
Bugu da kari, babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Nabil el-Araby ya bayyana cewa, kungiyarsa na goyon bayan kasar Sudan kan kokarin da ta yi wajen samun zaman karko da ci gaban kasar, kuma tana fatan za a iya warware rikicin kasar daga tushe ta hanyar yin shawarwari. (Maryam)