Bom da farko, ya tashi ne a kusa da wani karamin ofishin 'yan sanda dake Kuje, wajen babban birnin kasar, yayin da mintuna 15 da tashin na farkon bom na biyun ya tashi a kasuwar garin, kamar yadda wata majiyar jami'an tsaro ta shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua.
Ka zalika, bom na uku ya tashi ne a tashar mota dake Nyanya a wajen birnin na Abuja, inda aka taba samun wani mumunan harin boma da ya kashe mutane masu yawa a shekarar da ta gabata.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA, ta ce tuni ta tura jami'anta domin daukar wadanda harin ya rutsa da su zuwa asibitoci a babban birnin.
Mai magana da yawun hukumar ta NEMA Manzo Ezekiel, ya ce duk da cewar boma bomai sun tashi ne ba kakkautawa, amma jami'an ba da agajin na ci gaba da gudanar da aikin su. (Ahmada Fagam)