in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana takaicinta game da kisan ma'aikatan wanzar da lafiya a CAR
2015-08-10 10:17:00 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya bayyana matukar bacin ransa game da yadda aka halaka 'yan kasar Rwanda biyar da ke aiki a tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko MINUSCA a takaice.

Kakakin tsaron Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne lokacin da daya daga sojojin Rwandan da ke aiki a tawagar ta MINUSCA ya bude wuta kan abokan aikinsa, inda nan take ya halaka biyar da ga cikinsu kana 8 suka jikkata kafin daga bisani ya harbe kansa.

Mambobin kwamitin sulhun sun mika sakonsu na ta'aziya da kuma jaje ga tawagar MINUSCA da gwamnatin Rwanda da kuma iyalan sojojin da aka kashe. Sun kuma bukaci da a gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.

A halin da ake ciki, mambobin kwamitin sulhun sun saka nanata kudurinsu na baiwa tawagar MINUSCA cikakken goyon baya don taimakawa gwamnatin rikon kwaryar kasar sauke nauyin da ke kanta na shimfida zaman lafiya da tsaro a kasar.

Shi ma a sakonsa, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana bakin cikinsa da kisan ma'aikatan da ke aikin samar da zaman lafiyar, inda ya mika sakon ta'aziya ga gwamnati da al'ummar Rwanda da kuma iyalan mamatan.

Tun a farkon shekarar 2013 ne fada ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, lokacin da 'yan tawayen Seleka galibinsu musulmai suka kwace mulki a kasar, lamarin da ya haifar da hare-hare daga mabiya addinin Kirista. Daga bisani ne kuma kasar Faransa da wasu kasashen Afirka suka tura dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa kasar bayan da mayakan Seleka suka hambara da shugaba Francois Bozize a watan Maris na shekarar 2013.

Tashin hankalin kasar ya tilastawa dubban daruruwan mutane barin gidajensu, baya ga wasu da dama da ke gudun hijira a kasashen makwabta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China