in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin wanzar da zaman lafiya na MDD ya karbi sabon rahoto na cin zarafin mata a CAR
2015-09-16 10:55:02 cri
A ranar Talatar nan tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya CAR wato MINUSCA ta karbi wani sabon rahoto na zargin yin lalata da mata wanda ake zargin wani ma'aikacin tawagar da aikatawa a ranar 12 ga wannan watan na Satumba.

A yanzu haka, alkaluman zarge zargen yin lalatar da cin zarafin mata da ake zargin ma'aikatan na MINUSCA da aikatawa a CAR sun kai 15, kuma ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Mai Magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya ce tuni MINUSCA ta sanar da mahukuntan kasar kuma ana cigaba da gudanar da bincike bisa dokar ofishin babban sakataren MDD na yaki da cin zarafin mata da tilasta yin lalata da su.

Dujarric ya ce MINUSCA ta yi Allah wadai tare da yin kakkausar suka kan duk wani yunkuri na yin lalata da mata wanda ake zargin ma'aikatan na MDD da aikatawa. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China