Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya bayyana bacin ransa game da zargin baya-bayan nan da ake yiwa ma'aikatan wanzar da lafiya da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na cin zarafin jama'a.
Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai, ya kuma ce Mr Ban din bai ji dadin wannan rahoto ba, don haka ya yi kira da a gudanar da cikakken bincike don zakulo wadanda suka aikata wannan danyen aiki don ganin an gurfanar da su a gaban kuliya.
Kungiyar kare hakkin dan-Adam ko Amnesty International a takaice dai ta yi zargin cewa, wasu ma'aikatan da ke aikin wanzar da zaman lafiyar sun bindige wani mutum da dansa kana suka yiwa 'yarsa mai shekaru 12 fyade a wannan kasa.
Yanzu dai ana fatan tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, za ta hanzarta gudanar da bincike kan wannan zargi ba tare da wata rufa-rufa ba.(Ibrahim)