in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nada mukaddashin shugaban rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya dake CAR
2015-08-15 14:30:34 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon a ranar Juma'ar nan ya nada Parfait Onanga-Anyanga dan kasar Gabon da ya zama mukadashin shugaban rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta MDD dake kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wato CAR, domin maye gurbin Babacar Gaye da ya yi murabus a kwanan baya sakamakon karofi da aka yi tayi.

A sa'i daya kuma Parfait Onanga-Anyanga zai zama wakilin musamman na babban sakataren MDD dake kula da batun CAR. Shi dai Parfait Onanga-Anyanga ya taba daukar kujerar jami'in diplomasiyya na kasar Gabon dake MDD, daga baya ya gudanar da ayyuka a hukumomin MDD. A cikin 'yan shekarun nan ya taba zama darektan ofishin MDD dake kasar Burundi, da kuma mai shiga tsakani na hedkwatar MDD kan matsalar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Boko Haram, da dai sauransu.

Sakamakon zarge-zargen da aka yi wa tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake CAR wato MINUSCA game da yi wa fararen hula fyade, a ranar 12 ga wata Ban Ki-moon ya bayyana cewa, ya riga ya bukaci Babacar Gaye da ya yi murabus, ya kuma umurce wata kungiya mai zaman kanta da ta yi bincike kan zarge-zargen, da kuma daukan matakan da suka dace kan MINUSCA a nan gaba.

An ce, a wannan wata na Agusta, ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MINUSCA sun yi fyade ga wata yarinya mai shekaru 12 a Bangui, babban birnin kasar ta CAR, kana suka kashe wani yaro da mahaifinsa. Ba wannan ne karo na farko ba da ake zargin tawagar akan yin fyade a ciki 'yan watannin da suka wuce. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China