A ranar Alhamis din nan 9 ga wata, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana matukar mamakinsa game da harin da aka kai ma ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a birnin Bangui na kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a safiyar wannan rana, abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya da jikkata wadansu guda 8.
Wadansu mutane ne da ba a sansu ba suka kai wannan mummunan harin a kan ayarin ma'aikatan wanzar da zaman lafiya a Bangui kamar yadda wata sanarwar da kakakin majalissar ya fitar ma manema labarai.
Wannan a cewar sanarwar shi ne karo na farko da ma'aikacin wanzar da zaman lafiya ya halaka a kasar tun karbar da ikon tafiyar da aikin daga hannun kungiyar wanzar da zaman lafiya dake karkashin tarayyar kasashen Afrika a ranar 15 ga watan satumbar bana.(Fatimah Jibril)