Lu Junqing shugaban shirin a bayanin shi lokacin kaddamar da shirin a Lusaka babban birnin kasar Malawi ya ce tsarin shirin da babu rufa rufa a ciki da gwamnatin kasar Sin ta kirkiro da shi ya saka kamfanoni da dama sun inganta kokarin su na bada gudunmuwa ga daukan nauyin dake wuyan su.
Yace babu wani sharadi da aka saka ma shirin,kawai yana bayyana tsananin kauna ne. An yi shirin a baya, a yanzu ma ana yi, kuma za'a cigaba da yi har abada.
An kammala tattaunawa game da shirin a kasashe 4 sannan kuma a Zambiya za'a fara aiwatar da shi bayan cimma yarjajeniyar hadin gwiwwa.
An fara shirin na HOPE ne a nahiyar ta Afrika, a shekara ta 2010 inda aka gina makarantu 23 a kasashen Kenya, Tanzaniya,Burundi da Rwanda wanda ya taimaka ma fiye da yara 10,000 shiga makaranta. Shirin dai na da niyyar taimakawa wajen samar da makarantu 1,000 a daukacin nahiyar.
Har ila yau a cikin shirin ana fatan al'ummomi daga ko ina cikin duniya zasu iya gani, cewa cigaban kasar Sin ba zai zama barazana ma kowa ba illa ma ya kawo farin ciki ga duniya, inji Mr Lu Junqing.
Kakakin Ma'aikatar ilimin bai daya na kasar Zambiya Hillary Chipango ta bayyana aniyar kasar a kan shirin tare da cewa gwamnati a shirye take ta ga cewa an fara shirin cikin hanzari da zaran an cimma yarjejeniyar hadin gwiwwa.(Fatimah Jibril)