Kamfanoni 100 ne ake sa ran za su halarci bikin, inda aka tanada sassa guda 4 da za a baje kayayyaki kamar injuna, motoci, kayayyakin laturoni na gadi da sauran kayayyakin yau da kullum.
Wakilin kasar Sin mai kula da harkokin cinikayya dake kasar Tanzania Lin Zhiyong ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a ranar Litinin game da bikin cewa, Sin za ta yi kokari tare da bangaren kasar Tanzania wajen yaki da satar fasaha da kayayyakin jabu, matakin da zai taimaka wajen samar da kayayyakin Sin masu inganci ga jama'ar kasashen Afirka.
Mr Lin yana fatan wannan biki zai kasance wani dandalin yin mu'amala da hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka, da kuma jama'ar kasashen Afirka, ciki har da kasar Tanzania kamar yadda suke fata.
Tun a shekarar 2012 ne ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin ta fara shirya bikin nune-nunen kayayyakin Sin a kasashen Afirka, bikin da ake gudanar wa a kowace shekara. (Zainab)