Mr. Shi ya bayyana hakan ne ga wani taron manema labaru, bayan kammala taron yini biyu game da harkokin zuba jari a Afirka, wanda bankin duniya, da bankin samar da ci gaba na Sin, tare da wasu cibiyoyin kudi suka yi hadin gwiwar shiryawa a birnin Addis Ababan kasar Habasha.
An dai kafa asusun CAD ne a shekarar 2007, domin fadada hanyoyin bunkasa zuba jarin kasar Sin a nahiyar Afirka. Kuma ya zuwa yanzu, asusun ya shigar da kudade har dalar Amurka biliyan 2.3, a wasu ayyuka 80, wadanda suka hada da na samar da ababen more rayuwa, da harkar noma, da makamashi, da samar da lantarki, da masana'antu a kasashen Afirka sama da 30.