Kamfanonin da Sinoma international engineering na Sin zai gina za'a yi su ne a kasashen da suka hada da Ghana, Habasha, Kwaddibuwa, Kamaru, Mali, Niger, Senegal, Zambiya da kuma Kenya.
Ana sa ran wadannan za su kara adadin metric tan miliyan 25 a wanda yanzu haka kamfanin Dangoten ke samarwa na kusan metric tan miliyan 50.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote wanda alkalumma suka nuna shi ne mafi arziki a Nahiyar Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya shaida ma manema labarai a birnin Ikko na Nigeriya a lokacin rattaba hannun ranar laraban nan cewa ana sa ran aikin gina kamfanonin samar da simintin za'a kamala su ne a cikin watanni 30 a kuma yi bikin bude su a kasar Kamaru.
Alhaji Aliko Dangote ya ce wannan aiki wani ci gaba ne da aka samu a shirin da kamfanin yake yi na kara yawan simitin da yake samarwa zuwa metrik tan miliyan 100 nan da shekara ta 2020. (Fatimah)