in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ragowar ma'aikatan lafiya na Najeriya dake kasashen Saliyo da Laberiya sun dawo gida
2015-09-30 10:41:25 cri
Kasar Najeriya ta karbi a ranar Talata da gungun karshe na ma'aikatan kiwon lafiyarta da suka fito daga kasashen Saliyo da Laberiya. Da yake karbar wannan tawaga a Abuja, babban birnin Najeriya, sakatare dindindin a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya, Linus Awute, ya bayyana matukar jin dadinsa kan cewa duk mutanen da aka tura a cikin wannan aiki sun dawo gida cikin koshin lafiya. Mambobin tawagogin kiwon lafiyar za su tsaya karkashin kulawar likitoci a tsawon 'yan kwanaki, domin binciken lafiyarsu, in ji mista Awute. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China