Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya Sam Adurogboye ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin kasar.
Kakakin ya ce, an kama jirgin ne saboda ya ceta dokokin sararin samaniya na Najeriya da kuma yin zirga-zirga a cikin kasar ba bisa ka'ida ba, wanda hakan ya sa aka ci tarar sa dala 20,000.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, har yanzu wadanda suka mallaki jirgi na biyu ba su bi umarnin haramcin da hukumar NCAA ta Najeriyar ta yi musu ba.
Bayanai sun nuna cewa, jirgin na G-RBEN yana gudanar da zirga-zirga da takardun iznin zirga-zirga na bogi tsakanin Abuja da Lagos kuma ba bisa ka'ida. (Ibrahim)