in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa dangantakar ta da Najeriya a bangaren raya al'adu
2015-09-16 10:27:48 cri
A ranar Talata nan, Mahukuntan kasar Sin sun tabbatar da cewar, kasar ta shirya tsab domin karfafa dangantakarta da Najeriya a bangaren raya al'adu.

Babban daraktan cibiyar raya al'dun kasar Sin Yan Xiangdong, shi ne ya tabbatar da hakan a yayin halartar taron manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, yayin halartar taron musayar al'adu tsakanin kasar Sin da Najeriya na shekarar 2015.

Ya kara da cewar musayar al'adu batu ne mai matukar muhimmanci kuma yana da matukar alfanu wajen sake karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta fuskar raya al'adu wacce aka kulla ta sama da shekaru 10.

Ya ce bikin zai nuna irin fasahar zane zanen kayan karau da kasar Sin ke da shi kuma zai yi matukar tasiri wajen karfafa huldar dake tsakanin kasashen 2 ta fuskar raya al'adu.

Yan, ya shedawa 'yan jaridu cewar, bana shekaru 44 ke nan da kulla huldar dake tsakanin Nageriya da kasar Sin. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China