Sojojin da suka yi juyin mulki sun tsare shugaban rikon kwarya Michel Kafando, a ranar Laraba, kafin daga baya su sake shi a ranar Jumma'a.
Masu ruwa da tsaki a fagen siyasa da kuma masu shiga tsakani na kungiyar ECOWAS da ma gamayyar kasa da kasa sun cimma na kada kuri'ar bada afuwa da dukkanin sojojin da suka yi juyin mulki na ranar Laraban da ta gabata. (Maman Ada)