Burkina Faso : Masu zanga zanga sun hana a gudanar da wani taron masu shiga tsakani
A kasar Burkina Faso, daruruwan masu zanga zanga ne suka hana a gudanar da wani taron masu shiga tsakani a ranar Lahadi a gidan otel din Laico dake birnin Ouagadougou, bayan da shugaban kasar Benin Yayi Boni ya bayyana a ranar Asabar da yamma cewa dukkan masu ruwa da tsaki za su yi taro a ranar Lahadi da safe domin sanar da wani sabon albishir ga duniya. Bayan sun cincirindo a kewayen otel din, jami'an tsaron dake ba da kariya ga fadar shugaban kasa (RSP) sun tarwatsa wadannan masu zanga zanga dake dauke da allunan dake kawo suka ga sabbin hukumomin kasar na kwamitin kasa domin demokaradiyya (CND), haka ma jami'an tsaron suntarwatsa 'yan jarida. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku