in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JNI ta ayyana ranar 23 ga watan Satumba a matsayin ranar babbar Sallah
2015-09-14 20:07:52 cri

Kungiyar Jama'atu Nasril Islam (JNI) a Najeriya ta ayyana ranar 23 ga watan Satumban wannan shekara a matsayin ranar babbar Sallah.

Kungiyar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa mai dauke da sanya babban sakataren kungiyar Khalid Aliyu wanda mai alfarma sarkin musulmi Sa'ad Abubakar ya fitar a jiya Lahadi.

Sanarwa ta kuma yi wa daukacin musulmai fatan alheri a sabon watan Dhul Hajj da ya kama a yau Litinin. Sannan ta bukaci musulmai da su azumci kwanaki 9 na farko na watan, musamman Azumin ranar Arafat.

Bugu da kari, sanarwar ta yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro a Najeriya da su dauki dukkan matakan da suka dace na ganin an ceto babban limamin masallacin jami'ar Najeriya da ke Nsukka Sheikh Adam Idoko da wasu suka sace.

Sanarwar ta kuma mika sakon jaje da kuma ta'aziyya ga iyalan wadanda hadarin masallacin harami da ke Makka ya rutsa da su

Daga karshe sanarwar ta yiwa daukacin musulmi da ke shirin fara aikin hajjin bana kammala Ibadar cikin nasara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China