Wasu kafofin tsaro da suka bukaci a sakaye sunayensu sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua cewa, an ji karar fashewar wasu abubuwa guda 4 a yammacin birnin duk da sojojin da aka jibge a birnin da ya kasance tungar mayakan Boko Haram.
Sai dai har yanzu babu wani karin bayani game da mutanen da suka mutu ko suka jikkata sakamakon wannan fashewa. (Ibrahim Yaya)