Mayakan kungiyar da dama wadanda suka nuna taurin kansu an hallaka su a arangama tsakanin su da sojojin abinda yasa sauran 'yan kungiyar suka mika wuya a garin da yayi suna wajen samar da kifi, kamar yadda kakakin rundunar sojin yankin Sani Usman Kukasheka yayi ma kamfanin dillanci labarai na Xinhua bayani.
Manyan hada hadar tattalin arziki da ciniki tsakanin kasashen Kamaru, Chadi, jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ma ita kanta Nigeriya yana gudana ne a wannan gari na Banki.