Wata majiyar hukumar ta ce an kai hari na farko ne misalin karfe 2 na dare agogon wurin a wani kauye dake kusa da garin Mora a lardin arewa mai nisa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mazauna kauyen guda 9, harin da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kai wa, kana suka kona wasu gidaje. Sannan bayan sa'a guda da harin farko sai kuma an kai hari na biyu kan dakarun gwamnatin kasar Kamaru da aka jibge a yankin dake kan iyaka da Najeriya, inda sojoji biyu suka mutu, kana motocin soja 4 da wasu motocin daukar kaya na jama'a suka lalace. (Sanusi Chen)