in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar na tsare da mayakan Boko Haram fiye da dubu daya
2015-09-10 09:49:56 cri
A yanzu haka, kasar Nijar na tsare cikin kasarta da mayakan Boko Haram fiye da dubu daya, in ji ministan cikin gida da tsaron jama'a na kasar, Massaoudou Hassoumi.

Tun kusan watanni bakwai, Nijar, da Chadi da kuma Kamaru, kasashen dake makwabtaka da Najeriya cibiyar wannan kungiyar ta Boko Haram, suke fama da hare haren kungiyar a kai a kai, tun daga sansanoninta dake Najeriya, wadanda kuma suka yi sanadiyyar mutuwa ko jikkata darururan fararen hula da sojoji.

A halin yanzu, jami'an tsaron FDS na kasar Nijar na samun nasarar dakile wadannan hare hare na kungiyar Boko Haram tare da taimakon sojojin Chadi.

Hukumomin Nijar sun sanar da cewa an kashe darururan mayakan Boko Haram. Har ila yau, kafa dokar ta bace a jihar Diffa tun a ranar 10 ga watan Febrairun da ya gabata, ta taimaka wajen baiwa jami'an tsaro damar yin bincike da sintiri, da ma kare wannan yanki daga hare haren Boko Haram yadda ya kamata, in ji wata majiya.

A cewar Massaoudou, har yanzu ana cigaba da gwabza fada a kudancin kasar Nijar mai iyaka da Najeriya.

Haka kuma, ministan ya sanar da shirin shirya wani taro a zauren MDD kan batun Boko Haram. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China