Wani ganau mai suna Bulama yusuf ya bayyana cewa, wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam na farko a cikin wani masallaci a unguwar Ajilari a birnin Maiduguri,fadar mulkin jihar Borno mai fada da tashin hankali, harin da ya halaka mutane 9 tare da jikkata wasu mutane 15.
Ya ce, mituna biyar bayan harin farko sai kuma wasu bama-baman suka tashi a unguwar Gomari inda nan ma mutane sama da 30 suka jikkata. Bayanai na cewa, motocin 'yan sanda na hukumar bayar da agaji sun kai wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya Kanar Sani Usman Kukasheka ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua aukuwar lamarin, sai dai bai yi wani karin haske game da harin ba. (Ibrahim)