A cikin jawabinsa, shugaba Joko ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, tattalin arzikin Asiya da Afirka ya bunkasa cikin sauri, wanda kuma yake taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar kasashen duniya. Ya ce, ko da yake ana cikin yanayi mai kyau na raya tattalin arzikin nahiyoyin biyu, amma ana ci gaba da fuskantar kalubaloli da dama, shi ya sa ana fatan kasashen Asiya da na Afirka su ci gaba da tayar da ra'ayin taron Bandung, su karfafa hadin gwiwa a fannonin zuba jari da cinikayya da sauransu a tsakaninsu.
A nasa bangare, mataimakin shugaban kasar Afrika ta kudu Cyrille ya furta cewa, a fannin raya tattalin arziki, kasashen Asiya sun cimma nasarar daidaita matsalar hada hadar kudi, shi ya sa saurin bunkasuwar tattalin arzikinsu ya fi na kasashen Afirka. Yanzu ana fama da matsalar karancin horaswa a fannin fasahohi da tarbiya a kasashen Afirka. Ana fatan kasashen nahiyoyin biyu za su kara hadin gwiwa tsakaninsu a wadannan fannoni.
A wannan rana, masu masana'antu sama da 480 daga kasashen Asiya da na Afirka sun halarci taron, inda suka yi shawarwari kan hadin gwiwa tsakaninsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya.(Fatima)